Kano: Hukumar Hisba ta samu wasu masu neman auren gata da cututtuka

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce an samu wasu dake ɗauke da cututtuka a cikin waɗanda ke neman a yi musu auren gata.

Mai magana da yawun  hukumar ta Hisbah, Lawan Fagge ya ce an gano wannan ne daga gwaje-gwajen da aka yi kafin auren.

Karanta Wannan: Kano: INEC ta janye ƙarar da ta ɗaukaka kan hukuncin kotu

Malam Lawan Fagge ya ce tuni an maye guraben wadannan mutane da wasu daban. Kuma hukumar Hisbah za ta taimaka wa waɗanda ke ɗauke da cututtukan da magunguna.

Kakakin na Hisbah ya kuma ce sun tantance masu neman aure kusan 5000, gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta aurar da mutane 1800.

Post masu alaƙa

Ba za mu dawo da tallafin man fetur ba —Fadar Shugaban Ƙasa

Za a miƙa ƴan Najeriya da ake zargi damfara zuwa Amurka

Kotun majistare ta fara sauraren shari’ar sojan gona mai mukamin CSP